Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu gwajin tsororuwar tsaunin Qomolangma sun sake komawa aiki bayan jinkiri sau 2 sakamakon rashin kyan yanayi
2020-05-25 12:57:53        cri

Wata tawagar Sinawa dake fatan kaiwa ga tsirin tsaunin Qomolangma, sun sake komawa sansanin aikin su a jiya Lahadi, bayan dage lokacin fara aikin auna tsirin tsaunin har karo 2, sakamakon rashin kyawun yanayi.

Yanzu haka dai kwararru a fannin lura da yanayi, da mota mai dauke da na'urar lura da sufurin sama, sun isa sansanin tsaunin na Qomolangma, domin samarwa tawagar hidimar da take bukata.

Bisa tsarin aikin da za su gudanar, tawagar mahaya tsaunin za su kai ga sansani na 1, a wani wuri mai tudun mita 7,028 a ranar Lahadi, kana su kai ga tsororuwar tudun tsaunin a ranar Laraba 27 ga watan Mayu.

Tun kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, Sinawa masu aikin safiyo sun fitar da mizani karo 6, dake bayyana awon da'ira, da binciken kimiyya game da tsauni na Qomolangma, inda a shekarar 1975 suka ce tsaunin na da tsororuwar tudun mita 8,848.13, yayin da a shekarar 2005 kuma, suka ce tudun ya kai mita 8,844.43. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China