Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harkoki a Wuhan sun koma yadda suke inda ta karbi bakuncin wasanni karo na farko bayan barkewar COVID-19
2020-06-26 10:47:47        cri

An gudanar da gasar "Salute to the Heroes" wanda ke nufin "jinjina ga gwaraza" a makon da ya gabata a birnin Wuhan na kasar Sin.

Mahalarta gasar 234 sun hada da jami'an lafiya da masu bada hidima da 'yan sanda da masu kai sakonni da masu aikin sa kai da injiniyoyi da magina, amma kuma an kira su da suna guda wato "Gwaraza" kuma dukkan 'yan wasan mazauna birnin ne da suka nuna jarumta yayin da ake yaki da cutar COVID-19 a watannin baya-bayan nan.

Wannan shi ne wasan motsa jiki na farko da aka yi a birnin tun bayan barkewar COVID-19 a watan Janairun bana. Sannu a hankali, harkoki na komawa yadda suke a birnin Wuhan, wanda a baya ya kasance inda cutar ta fi kamari.

An gudanar da gasar ne a babban dakin wasan motsa jiki na Wuhan, wanda aka mayar asibitin tafi da gidanka a watan Fabreru, da ya kwantar da masu cutar COVID-19 sama da 300.

A cewar Xu Yibin, daraktan dakin wasan, an gudanar da feshin maganin kashe kwayoyin cuta sau da dama a dakin.

Kididdigar hukumar kula da wasanni ta Wuhan, ta nuna cewa, a yanzu, sama da kaso 70 na wuraren wasanni a birnin sun bude. Kuma adadin masu zuwa wuraren ya tsaya akan kaso 80 na adadin da aka samu a bara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China