Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen kungiyar EAC za su samar da dabarun farfado da bangaren yawon bude ido bayan COVID-19
2020-06-24 11:08:35        cri
Kasashe mambobin kungiyar raya yankin gabashin Afrika, za su aiwatar da wasu dabaru domin bunkasa farfado da bangaren yawon bude ido, watanni bayan koma bayan da bangaren ya samu saboda annobar COVID-19.

Mataimakin sakatare janar na sashen kula da ayyuka da harkokin jama'a na kungiyar, Chritophe Bazivamo, ya ce, kungiyar na tattaunawa da gwamnatoci da kamfanoni domin samar da hadaddiyar dabarar farfado da bangaren.

Ya ce kasashe mambobin kungiyar, na hasashen ya zuwa watan Yuli, tafiye tafiye bude ido za su ragu da kaso 60, yayin da yawan masu cutar zai ragu, wanda zai kai ga sassauta matakan dakile cutar da aka dauka, kamar na rufe iyakoki.

Ya ce rashin kudin shiga a bangaren yawon bude ido a yankin, ya kai ga rage ma'aikata, da kuma dakatar da aiwatar da wasu ayyukan kiyaye namun daji, da za su samar da kudin shiga ga al'ummomin karkara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China