Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakiyar firaministan Sin ta jaddada bukatar zage damtse wajen yaki da COVID-19 a Beijing
2020-06-24 11:03:56        cri

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan, ta jaddada bukatar zage damtse, a yakin da ake yi da cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Beijing.

Sun Chunlan ta yi kiran ne a jiya Talata, tana mai cewa, ya zama wajibi a kara azama wajen daukar matakan kandagarki, da shawo kan wannan annoba, ta yadda da a iya dakile bazuwar cutar a birnin.

Sun wadda ta ziyarci wasu sassa na birnin, ta kuma zanta da mazauna unguwanni, da kuma leka wasu wurare da asibitoci, ta nazarci irin matakan da ake dauka, da yanayin jiyyar da ake baiwa masu dauke da cutar, da sauran muhimman matakan da ake dauka.

Jami'ar ta ce, duk da cewa an shawo kan bullar cutar dake da alaka da kasuwar kayan lambu ta Xinfadi, akwai karin masu dauke da ita a cikin iyalai da wasu ma'aikata, ana kuma samun bazuwar ta a wasu unguwanni. Don haka jami'ar ta ce, yanzu ba lokaci ne da za a yi sakwa-sakwa da matakan da ake dauka ba.

Daga nan sai ta jaddada bukatar kara inganta cikakken tsarin gudanar da gwaji, ajiyewa da sufuri, tare da gabatar da bayanan sakamakon cutar. Kaza lika ta jaddada muhimmancin fadada damar gwada al'umma, ko a kai ga komawa bakin ayyuka, da ma sauran harkokin rayuwar yau da kullum kamar yadda aka saba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China