Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa kan yadda Trump ya kira COVID-19 "Kung Flu"
2020-06-22 20:01:53        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasarsa na nanata adawar dake kan yadda ake amfani da COVID-19 wajen nuna wariya, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya kira kwayar cutar da sunan "Kung Flu" .

Zhao ya shaidawa taron manema labarai da aka saba gudanarwa cewa, hukumar lafiya ta duniya da ma al'ummomin kasa da kasa sun bayyana adawarsu da alakanta cutar da wata kasa ko yanki da ma duk wani nau'in nuna wariya.

Ya ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau'i na nuna kyama ga asalin cutar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China