Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin HK: Har yanzu HK wuri ne da kamfanonin kasashen waje za su samu ci gaba
2020-06-24 10:56:36        cri
Kantoman yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, Madam Carrie Lam, ta ce bayan zartar da dokar tsaron kasa a HK, yankin zai ci gaba da kasancewa wurin da kamfanonin kasashen waje za su samu ci gaba.

Yayin wani taro kan raya kasar Sin da aka yi ta kafar intanet, Carrie Lam ta ce tana sane cewa, babban abun damuwa ga kamfanonin kasashen waje shi ne, ko za su rayu a yankin, inda ta bayyana cewa, amsarta ita ce "eh"

Ta ce dokar na mayar da hankali ne kan ayyukan ta'addanci, da na neman ballewa, da raina ikon gwamnati, da hada kai da baki domin illata tsaron kasa, tana mai cewa, a bayyane yake cewa, wadannan ba ayyuka ne na kamfanoni ko mazauna masu kiyaye doka ba.

Ta ce ya kamata galibin mutane, ciki har da kamfanoni masu kiyaye doka, su yi maraba da dawowar zaman lafiya da doka da oda, wadanda suka mayar da yankin HK daya daga cikin birane mafi aminci a duniya cikin shekaru da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China