Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya bukaci kasashen Sin, Rasha da Indiya su yi aiki tare
2020-06-24 10:24:30        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taro ta kafar bidiyo a ranar Talata tare da takwarorinsa ministocin kasashen Rasha da Indiya, inda ya bukaci kasashen uku da su aika da kyakkyawan sako ga sauran kasashen duniya ta hanyar yin hadin gwiwa da junansu wajen yaki da annobar COVID-19, da bunkasa tattalin arziki gami da kiyaye dokokin kasa da kasa.

Wang ya ce, kasashen Sin da Rasha da Indiya dukkansu manyan kasashe ne dake kiyaye matsayin 'yancin kai. Kamata ya yi kasashen su yi cikakken la'akari da yanayin da ake ciki don yin hadin gwiwa a matsayinsu na abokan hadin gwiwar juna domin samar da damammaki ga kowane bangare, kuma su zartar da kudurori da nufin taimakawa kasashen uku wajen cimma nasarar bunkasuwa da kawo sauye-sauye kana da ceto zaman lafiyar duniya da ci gaba duniyar baki daya.

Ya kamata su mayar da hankali wajen mu'amalar juna bisa ingantaccen tsari wanda zai kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen, da kuma ceto dukkannin yanayin da ake ciki game da dangantakar dake tsakaninsu.

Ya ce a wannan shekara ake cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu da kuma kafa MDD, Wang ya bukaci kasashen uku da su kiyaye alfanun dake tattare da nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu. Ya kamata su yi watsi da duk wani abu da zai iya mayar da hannun agogo baya a bisa tarihi, su nuna adawa da duk wani mataki na nuna mulkin danniya, da yin babakere a tsarin siyasa, kana su yi kokarin goyon bayan bunkasa demokaradiyya da karfafa goyon bayan dangatakar dake tsakanin kasa da kasa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China