Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta sake nanata aniyyarta wajen yaki da yunkurin kasashen ketare na tsoma baki a harkokin Hong Kong
2020-05-27 19:39:41        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya sake nanata cewa, batun kafa dokar kiyaye tsaron kasa na yankin musamman na Hong Kong batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, don haka kasashen ketare ba su da ikon tsoma baki a cikinsa, kuma kasar Sin tana nan a kan bakarta ta adawa da yunkurin duk wata kasar ketare, na tsoma baki a harkokin Hong Kong.

Zhao Lijian ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Laraba.

Kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Laudio-videorov ya bayyana cewa, kalaman Amurka game da saka takunkumi kan kasar Sin saboda nazarin dokar tsaron kasa ta Hong Kong da majalisar wakilan jama'ar kasar ke yi, ta nuna isa, da yadda Amurka ke abubuwa da gangan, kuma hakan ba zai shafi tattaunawar dake tsakaninta da Sin kan sauran batutuwa ba.

Da yake karin haske kan wannan tambayar da aka yi masa, Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasar Sin ta amince da kuma nuna yabo sosai kan ra'ayin minista Sergei Laudio-videorov, abin ke nuna kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha. Ko da yaushe kasashen biyu na nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu.

Game da kalaman Amurka na saka takunkumi kan kasar Sin, Zhao Lijian ya jaddada cewa, duk wata kasar dake da neman lahanta moriyar kasar Sin, to Sin za ta dauki matakan da suka wajaba don mayar da martani. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China