Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taya Burundi murnar shirya babban zaben kasar
2020-05-27 19:05:51        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, kasar Sin ta taya kasar Burundi murnar shirya babban zaben kasar cikin nasara, tana kuma martaba zaben da jama'ar Burundi suka yi, kana tana fatan ganin za a kara samun sabon ci gaba kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka gudanar yau Laraba a nan birnin Beijing.

Rahotanni na cewa, a ranar 25 ga wata ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Burundi ta sanar da kashin farko na sakamakon zaben shugaban kasar, inda aka ayyana cewa, dan takarar jam'iyyar CNDD-FDD dake mulkin kasar Evariste Ndayishimiye ya samu sama da kashi 68 cikin 100 na kuri'un da aka kada, abin da ba shi rinjaye sosai a zaben. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China