Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba ta da ra'ayin tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe
2020-06-10 20:36:53        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa, tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, ko kadan ba ya cikin tsarin manufar diflomasiyar kasar Sin kuma ba ta iya haka ba.

Madam Hua ta bayyana haka ne a Larabar nan a birnin Beijing, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Rahotanni na cewa, wata cibiyar tsara muhimman dabaru ta kasar Australia ta fitar da wani rahoto dake cewa, wasu hukumomin kasar Sin sun yi amfani da wasu dubban kungiyoyi wajen tattara wasu bayanan sirri, don gamsar da Sinawa dake ketare da ma wasu kasashe kawayenta, kan yadda za su yayata muradun kasar ta Sin. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China