Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin Afirka da kwararru sun jinjinawa jawabin shugaba Xi
2020-06-18 09:56:50        cri

Jagororin Afirka, da kwararru a fannin kiwon lafiya, sun jinjinawa jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin taron musamman na Sin da kasashen Afirka game da yaki da cutar COVID-19, wanda ya gudana jiya Laraba ta kafar bidiyo.

Shugabannin Afirka, ciki hadda na kasashe mambobin kungiyar AU, da shugabannin karba karba na manyan hukumomin yankunan nahiyar, da ma shugaban hukumar zartaswar AUn, sun halarci wannan taro da Sin ta karbi bakunci, inda suka nuna yabo game da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin yaki da wannan cuta.

Da yaka gabatar da jawabi yayin taron, jagoran kungiyar AU, kuma shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce "Wannan taro na musamman, ya nuna zurfin cudanyar Sin da Afirka."

A nasa jawabin, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya jinjinawa kasar Sin, da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da hukumar lafiyar ta kasa da kasa WHO, wadanda kwazon su, da matakan da suka dauka ke taimakawa kasashe masu tasowa dake nahiyar Afirka wajen shawo kan wannan cuta.

Buhari ya ce tallafin Sin, ya yi matukar karfafa himmar kasar sa, na dakile cutar COVID-19. Kaza lika taimakon shugaba Xi ya kara nuna irin hadin gwiwa mai ma'ana, da alaka mai nagarta da ta jima tsakanin kasashen dake halartar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC.

Shi kuwa mashawarcin shugaban janhuriyar Nijar a fannin tattalin arziki da zamantakewa da al'adu Boubacar Abdou, cewa ya yi, Sin ta taka rawar gani a fannin yaki da cutar COVID-19 a dukkanin fadin duniya, musamman ma a Afirka, karkashin manufarta ta tallafawa dukkanin sassa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China