Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin za su yi hadin gwiwar kafa cibiyar zakulo albarkatun ruwa a Angola
2019-12-25 13:02:19        cri

Kamfanonin kasashen Sin, Portugal, da Koriya ta kudu za su yi hadin gwiwa wajen gudanar da aikin kafa cibiyar samar da nau'ikan albaratun cikin teku a arewacin lardin Zaire na kasar Angola.

Daraktan ofishin hukumar kula da aikin gona, kiwon dabbobi da kamun kifi na kasar Angola Gouveia Pedro, shi ne ya sanar da shirin.

Za'a aiwatar da aikin ne a shekarar 2020 a Mukula, wato yankin gabar tekun Tomboco dake lardin Zaire.

Tekun Mukula yana da dubun albarkatun ruwa da suka hada nau'ikan kifaye iri daban daban.

A cewar Pedro, shirin ya kunshi gina gidajen kwana ga ma'aikatan da za su gudanar da shirin, kuma aikin zai samar da guraben ayyukan yi sama da 2,000.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China