Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Angola: Takaddamar dake tsakanin Sin da Amurka na kawo babbar illa ga tattalin arzikin Afrika
2019-06-28 10:42:36        cri

Shugaban sashen kula da harkokin ketare na jam'iyyar MPLA ta kasar Angola a takaice, Mista Maquento Sebastian Lopes ya shedawa 'yan jaridar CRI cewa, takaddamar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, kasashe mafiya karfin tattalin arziki, za ta kawo babbar illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ciki hadda kasashen Afrika da ma kasar Angola.

A cewarsa, a halin yanzu, Sin ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki baya ga Amurka, saboda haka Amurka ba ta son ganin bunkasuwar Sin cikin sauri ko kadan. Amurka ta tayar da takaddamar ciniki da kasar Sin ne da zummar hana bunkasuwar kasar Sin. A ganinsa, takaddamar ba kawai za ta kawo illa ga bunkasuwar kasashen biyu ba, har ma za ta yi mummunan tasiri ga ci gaban sauran kasashen duniya ciki hadda kasashen Afrika. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China