Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Angola ya kaddamar da filin jirgin saman da kasar Sin ta gina
2019-10-19 16:10:14        cri
Shugaban Angola Joao Lourenco, ya kaddamar da filin jirgin sama na Kuito, wanda kasar Sin ta gina a lardin Bie na kasar.

Tun a shekarar 2017 rukunin kamfanin China Railway 20th wato CR20, ya gina filin, wanda daya ne daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Angola kuma muhimmiyar cibiyar sufurin jiragen sama a yankin Bie.

Yayin bikin kaddamar da filin jirgin saman, Si Qin, jami'in yada labarai na aikin ginin, ya ce ayyukan filin jirgin saman sun hada da ginin sabon dakin zama na fasinjoji da na muhimman mutane da ginin wurin kula da zirga-zirgar jiragen sama da kuma wurin saukewa da loda kayayyaki.

Si Qin, ya ce kamfanin CR20 ya dauki daruruwan ma'aikata a yankin, sannan ya horar da sama da ma'aikata 400 da ke aikin kawata wuri da sarrafa injuna da masu aune-aune, wanda ya kara yawan ma'aikata da inganta yanayin zaman rayuwar al'ummar yankin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China