Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta martaba kwazon Sin a fannin bunkasa hadin gwiwar yakar COVID-19 in ji ministan harkokin wajen kasar
2020-06-22 11:08:57        cri

Ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry, ya jinjinawa kwazon kasar Sin, gama da bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa da take yi, wajen yakar cutar numfashi ta COVID-19.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Sin dake Masar ya fitar, ta rawaito Shoukry na wannan tsokaci da yammacin jiya Lahadi, yayin zantawarsa da jakadan Sin a Masar Liao Liqiang, lokacin da jami'an biyu suka tattauna alakar kasashen su, da managarcin hadin kai dake tsakanin sassan biyu.

Mr. Shoukry ya ce kwarewar Sin a fannin yaki da wannan annoba, ya cancanci daukacin kasashen duniya su yi koyi da shi. Kaza lika ita ma Masar na fatan ci gaba da aiki tare da Sin, wajen zurfafa alakar kasar da nahiyar Afirka, da ma kara kyautata hadin gwiwar sassan biyu. Ya ce Sin da Masar suna tare, a yakin da ake yi da wannan annoba, ta hanyar musayar kayayyakin tallafi da na kwarewar aiki.

A farkon watan Fabarairu, Masar ta samar da tallafin yaki da cutar COVID-19 ga kasar Sin, kana daga bisani ita ma Sin ta rama wannan alheri ta hanyar turawa Masar din kayayyakin tallafi har karo uku, ciki hadda wanda kasar ta karba a tsakiyar watan Mayu.

Tun daga tsakiyar watan Afirilu zuwa yanzu, likitocin Sin da kwararru a fannin kiwon lafiya, sun gudanar da taro ta kafar bidiyo har sau uku da takwarorin su na Masar, a wani mataki na musayar kwarewa a fannin kandagarki da magance cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China