Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Trump ya sa hannu kan umurnin tabbatar da tsaron 'yan sanda a bakin aiki
2020-06-17 15:34:05        cri

Jiya Talata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan umurnin tabbatar da tsaron 'yan sanda yayin da suke bakin aikin.

Bisa wannan umurni mai suna "Tabbatar da tsaron unguwanni bisa ayyukan 'yan sanda yadda ya kamata", dole ne hukumomi masu aiwatar da doka daban-daban na jihohin kasar su kimanta da kuma kyautata matakai da kuma manufofinsu don tabbatar da gudanar da ayyukansu a fili da tabbatar da tsaro da kuma sauke nauyin dake wuyansu. Don haka, ma'aikakar doka da shari'a za ta tsai da ma'auni da kafa wata hukuma mai zaman kanta, da kuma baiwa hukumomin da za su nemi takardar shaidu daga hukumar kudi, don kara musu kwarin gwiwa..

Shugabar majalisar wakilan Amurka kuma mambar jam'iyyar Demokuradiyya Nancy Patricia Pelosi ta ba da wata sanarwa a wannan rana, inda ta yi zargin cewa, wannan umurni ba shi da karfi, kuma ba zai kawar da ra'ayin bambancin launin fata da kawo karshen karfin tuwo da 'yan sanda suke nuna wa Amurkawa bakar fata ba, matakin da ya yi sanaddiyar mutuwar bakaken fata da dama a kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China