Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai alaka tsakanin bayanan bogi da suka samo asali daga Twitter game da annobar COVID-19 da masu goyon bayan Trump da kungiyar QAnon
2020-06-09 10:57:17        cri
Rahoton nazari na wata cibiyar bincike ta kasar Australia dake da mazauni a Canberra, ya nuna cewa, akwai alaka ta kut-da-kut tsakanin bayanan bogi da aka yayata a kafar Twitter yayin da ake fama da COVID-19 da masu goyon bayan shugaba Trump da kuma kungiyar QAnon.

Rahoton mai taken "kamar kwayar cuta: tsara yaduwar bayanan bogi game da COVID-19" ya gano cewa, kimanin rukunoni 30 na masu amfani da shafin Twitter dake da alaka da magoya bayan shugaban Amurka Donald Trump, da jam'iyyar Republican ko kuma kungiyar QAnon, sun yada jita-jitar dake cewa COVID-19 makami mai guba ne da aka kirkiro a kasar Sin.

QAnon kungiya ce ta masu rajin yayata boyayyun manufofin adawa da gwamnatin Trump da magoya bayansa

An fara yada jita jitar dake cewa gwamnatoci daban daban ne suka kirkiro COVID-19 a matsayin wani bangare na gwajin ayyukan soji, a kafar sada zumunta a farkon watan Fabreru, wadda hukumar lafiya ta duniya da sauran kungiyoyi masu bincike suka musanta. Hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka da jami'an lafiya na kasar ma sun amince cewa ba dan Adam ne ya kirkiro kwayar cutar ba.

Masu binciken sun bayyana cewa, ko ma dan Adam ne ya kirkiro cutar, sun gano cewa wadancan kungiyoyi ne suke yadawa da kansu, ko kuma wasu mutane ne na daban suka yada domin sauya tunanin duniya game da kungiyoyin, suna masu cewa, tasirin dai daya ne, wato bayanan da wasu ke yadawa ta hanyoyin da ba su dace ba, ka iya yaduwa a cikin al'umma tare da samun karbuwa da sahihanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China