Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton dake cewa wai an rushe masallatai da karfi a Xinjiang ba shi da gaskiya ko kadan
2020-06-20 17:26:01        cri

A kwanakin nan akwai wasu rahotannin dake nuna cewa, wai an rushe masallatai da karfi a jihar Xinjiang ta kasar Sin. Game da hakan, darekan kwamitin kula da harkokin kabilu na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai, Mehmut Usman ya bayyana cewa, wadannan rahotannin ba su da gaskiya ko kadan.

Hukumomi a jihar Xinjiang na nuna kwazo wajen samar da tabbaci ga mabiya addinin Musulunci don su gudanar da harkokin ibada yadda ya kamata, da maida hankali sosai ga karewa gami da gyara masallatai daban-daban, kuma akwai wasu masallatai a jihar wadanda aka gina su a shekarun 1980 zuwa 1990. Sakamakon ci gaban birane da garuruwa gami da bunkasuwar yankunan karkara, gwamnatin jihar Xinjiang tana kokarin daukar matakai daban-daban domin sake gyara wasu masallatai, wadanda suka riga suka tsufa ko suka lalace, domin biyan bukatun mabiya addinin Musulunci, da saukaka musu ayyukan ibada da salloli, al'amarin da ya samu babbar karbuwa daga malaman bangaren addini gami da mabiya addinin Musulunci a wurin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China