Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
kasar Sin ta yi Allah wadai da shirin dokar kare hakkin bil-Adam ta Uygur ta shekarar 2020 da Amurka ta sanyawa hannu
2020-06-18 20:16:30        cri
Kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya yi Allah wadai da ma adawa matuka, kan matakin Amurka na sanya hannu kan shirin dokar kare hakkin bil-Adam ta Uygur ta shekarar 2020 .

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da ya fitar Alhamis din nan, kwamitin ya bayyana cewa, matakin na Amurka, tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ya saba muhimman ka'idojin da suka shafi hadin gwiwar kasa da kasa.

Shi ma kwamitin kula da harkokin waje na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya bayyana rashin amincewarsa gami da nuna adawa kan wannan mataki na Amurka na sanya hannu kan wannan doka.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar jihar Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa, ya yi Allah wadai da kakkausar murya da nuna adawa kan sanya hannun da Amurka ta yi kan wannan doka game da Xinjiang.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China