Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Xinjiang zai zuba sama da Yuan biliyan 2 wajen gina tashoshin 5G
2020-06-08 20:44:23        cri

Rahotanni daga yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin na cewa, yankin yana shirin zuba zunzurutun kudi har sama da Yuan biliyan biyu, kwatankwacin dala miliyan 282, don gina tashoshin sadarwa na 5G kimanin 4,900 a wannan shekara.

Ya zuwa karshen wannan shekara, ana sa ran yankunan biranen Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang zai ci gaba da samun hidimomin 5G, yayin da sauran yankuna da birane su ma za su ci gaba da amfana da tsarin na 5G. A halin yanzu ana amfani da fasahar 5G wajen jinyar kula da lafiya ta kafar bidiyo da kula da na'urorin tashar samar da wutar lantarki da na'urorin hakar ma'adinai masu sarrafa kansu da sauran fannoni a yankin na Xinjiang. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China