Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen kasa da kasa sun yabawa taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da COVID-19
2020-06-19 14:35:52        cri


A ranar 17 ga wata, an yi taron kolin kasashen Sin da Afirka na musamman kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 ta kafar bidiyo. A wannan muhimmin lokacin da kasar Sin da kasashen Afirka suke hada kansu wajen yaki da annobar, kasar Sin, da kasar Afirka ta Kudu, wato shugabar kungiyar tarayyar kasashen Afirka(AU) a wannan karo, da kasar Senegal, wato shugabar dandalin tattaunawa hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) sun yi kira cikin hadin gwiwa domin gudanar da wannan taro, lamarin da ya nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakanin al'ummomin Sin da Afirka, da aniyarsu ta karfafa hadin gwiwar yaki da COVID-19 a wannan lokaci na musamman.

Ga karin bayani daga Maryam Yang…

Manyan shugabannin kasashen Afirka sun halarci wannan taro, inda suka nuna yabo matuka game da hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da cutar COVID-19. Kuma shugabannin da suka halarci taron sun hada da, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, shugaban kasar Congo(Kinshasa) Felix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, shugaban kasar Algeria Abdelmajid Tebboune, shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, da kuma firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali.

Bayan taron, fadar shugaban kasar Kenya ta fidda wata sanarwa cewa, Sin da Afirka suna cikin hadin gwiwa wajen goyon bayan hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da kin siyasantar da batun annoba. Sa'an nan, kasashen Ruwanda da Algeria da sauransu sun fidda wata sanarwa, inda suka yaba matuka kan hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da COVID-19.

Shugaban kungiyar hadin gwiwa da bunkasuwar Sin da Afirka ta kasar Morocco Nasser Bouchiba ya bayyana a ranar 17 ga wata cewa, taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 da aka kira ya nuna ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar ayyukan likitanci da kiwon lafiya, gudanar taron ya ba da muhimmanci wajen ginawa da kuma kyautata tsarin kiwon lafiyar jama'a a kasashen Afirka.

Haka kuma, yana ganin cewa, tabbas za a cimma nasarar yaki da cutar, idan akwai hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A nan gaba kuma, al'ummomin Sin da Afirka za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su samar da karin damammaki, da kuma samun ci gaba tare.

Tsohon jami'in diflomasiyya na ma'aikatar harkokin hadin gwiwa da dangantakar kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu Gert Grobler ya bayyana a ranar 17 ga wata cewa, taron da aka gudana ya nuna kyakkyawan zumunci da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasa da kasa, Sin da Afirka sun karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu. A nan gaba kuma, shirin "ziri daya da hanya daya" zai kasance muhimmin tushen farfado da tattalin arzikin kasa da kasa.

Haka kuma, ya ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin da kasashen Afirka sun karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa ka'idojin girmama juna, taimakon juna da fahimtar juna, domin cimma moriyar juna. A halin yanzu kuma, an zurfafa zumunci da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a fannonin kiwon lafiya, da farfadowar tattalin arziki da kuma hadin gwiwar kasa da kasa. Ya ce, Sin da Afirka suna bukatar goyon baya daga juna, hadin gwiwar dake tsakaninsu ba kawai tallafawa bangarorin biyu za ta yi ba, har ma da taimakawa dunkulewar dukkanin bil Adama.

A halin yanzu, kasashen Afirka suna dukufa wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, a sa'i daya kuma, suna gaggauta farfado da tattalin arzikinsu. Shugaban kwalejin nazarin shirin "ziri daya da hanya daya" na jami'ar horar da malamai ta Beijing Hu Biliang ya bayyana cewa, za a iya raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta hanyar zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, bisa tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka, ta yadda za a rage hasarar da matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar ga tattalin arzikin kasashen Afirka.

Masanin kwalejin nazarin harkokin Afirka na jami'ar horar da malamai na lardin Zhejiang Chen Li ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin duniya, kasar Sin ta dauki nauyinta a matsayin wata babbar kasa, tana hadin gwiwa da kasashen Afirka a ko da yaushe, domin karfafa dunkulewar Sin da Afirka, lamarin da ya kasance abin koyi ga dunkulewar dukkanin bil Adama. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China