Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rantsar da Evariste Ndayishimiye a matsayin sabon shugaban Burundi
2020-06-19 11:30:59        cri
Sabon shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye, wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 20 ga watan Mayu, a jiya Alhamis ya sha rantsuwar kama aiki a babban birnin kasar Gitega dake tsakiyar Burundi.

Sabon shugaban kasar, ya karbi ragamar shugabancin kasar bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Pierre Nkurunziza, wanda ya mutu a ranar 8 ga watan Yuni. Shugaban ya yi alkawarin hada kan al'ummar kasar, da daga matsayin kare hakkin dan adam, kamar yadda ya bayyana a jawabinsa na farko bayan ya sha rantsuwar kama aiki.

Ya bukaci dukkan 'yan kasar Burundi dake gudun hijira da su koma kasarsu, domin su ba da gudunmawa wajen cigaban kasar.

Ya ce za a nunawa al'ummar duniya cewa, kasar Burundi za ta iya bada gudunmawa ga cigaban duniya, ya kara da cewa, kasar ta shiyyar tsakiyar Afrika kofarta a bude take ga dukkan kasashen duniya dake sha'awar yin hadin gwiwa tare da kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China