Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zababben shugaban kasar Burundi zai kama aiki biyo bayan mutuwar shugaba Nkurunziza
2020-06-13 15:33:34        cri
Kotun kundin tsarin mulkin Burundi, ta sanar da cewa, za ta rantsar da zababben shugaban kasar Evariste Ndayishimiye nan ba da dadewa ba, bayan mutuwar shugaba Pierre Nkurunziza.

A baya, an sa ran Evariste Ndayishimiye, wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 20 ga watan Mayu, ya karbi ragamar mulki daga hannun Pierre Nkurunziza a watan Augusta, lokacin da wa'adin mulkinsa zai kare. Sai dai, mutuwar Nkurunziza a ranar Litinin sanadiyyar bugun zuciya, ya ba shugaban majalisar dokokin kasar, Pascal Nyabenda, damar zama shugaban rikon kwarya kafin rantsar da zababben shugaban, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Taron majalisar ministocin kasar da aka yi a ranar Alhamis, ya yanke dauki matakin tuntubar kotun kundin tsarin mulkin kasar, domin yanke shawara game da gurbin da aka samu bisa kundin tsarin mukin.

Shugaban kotun Charles Ndagijimana, ya bayyana a Bujumbura, babban birnin kasuwanci na kasar cewa, kotun ta lura da gurbin da aka samu, kuma tuntubarta da aka yi, ya yi daidai. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China