Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata kwamitin tsaron MDD ya sake duba na tsanaki game da ci gaban yanayin tsaro a Burundi, in ji wakilin Sin
2019-10-31 10:26:05        cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce kamata ya yi kwamitin tsaron MDD ya yi duba na tsanaki, game da ci gaban da kasar Burundi ta samu a fannin wanzar da zaman lafiya, da shirin ta na gudanar da zabuka.

Wu Haitao, ya ce yayin da kasar ke fuskantar babban zaben ta na shekarar

2020 mai zuwa, an samu ci gaba sosai a fannin komawar 'yan gudun hijira zuwa gida. Kaza lika yanayin tsaron kasar na kara inganta. Baya ga ci gaba da kasar ke samu a dukkanin fannoni.

Daga nan sai ya yi kira ga kasashen duniya da su martaba jagorancin kasar Burundi, da muradun al'ummar kasar game da zabukan dake tafe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China