Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaron Burundi sun kashe 'yan bindiga 14 a arewa maso yammacin kasar
2019-10-23 10:08:56        cri
An kashe a kalla 'yan bindiga 14 da suka shiga Burundi daga Jamhuriyar demokuradiyyar Congo jiya da asuba, biyo bayan bata-kashin da suka yi da jami'an tsaro a arewa maso yammacin Burundin.

Mataimakin kakakin ma'aikatar tsaron Burundi, Moise Nkurunziza, ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, mazauna kauyen Kayange na gundumar Musigati dake lardin Bubanza, da suka ga wata tawaga ta 'yan bindiga 18 sun shiga kauyen daga Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ne suka sanar da jami'an tsaro.

Moise Nkurunziza, ya ce jami'an tsaron sun kashe mutum 14 daga cikinsu tare da kwace bindigogi 11.

Sai dai rundunar 'yan sandan ba ta bayyana ko su wanene maharan ba, amma wata kungiyar 'yan tawaye dake rajin dawo da doka da oda a kasar, da ake zargin na da mazauni Jamhuriyar demokuradiyyar Congo, ta dauki nauyin kai harin a shafinta na Twitter. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China