Game da sake samun cutar COVID-19 a birnin Beijing na kasar Sin, shugabar kula da fasahohin ayyukan kiwon lafiya cikin gaggawa ta hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Maria Van Kerkhove ta bayyana a jiya cewa, an riga an kaddamar da tsarin magance yaduwar cutar a birnin Beijing. Kafin wannan, an samu irin yanayin a kasashen Singapore, Japan, Jamus da sauran kasashe. Ana bukatar kowa ya shirya tinkarar cutar, da gano wadanda suka kamu da ita cikin sauri, da jinyar su, da kuma neman wadanda suka yi mu'amala da masu cutar. Game da kasashen da suka cimma nasarar hana yaduwar cutar ko kusan cimma nasarar hana yaduwar cutar, ya kamata su shirya sosai don gano cutar idan ta sake barkewa, tare da kashe kwayoyinta cikin hanzari.
Shugaban kula da ayyukan kiwon lafiya cikin gaggawa na hukumar WHO Michael Ryan ya bayyana cewa, a cikin watanni shida da suka gabata, Sin ta samu fasahohi da dama wajen yaki da cutar COVID-19, kuma hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin, suna kokarin bincike da magance yaduwar cutar a wannan karo, kana hukumar WHO za ta ci gaba da hadin gwiwa da kasar Sin da ba ta goyon baya.(Zainab)