Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: 'yan Afrika da suka kamu da cutar COVID 19 ba su da yawa
2020-05-26 13:26:20        cri

Babban sakataren WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a jiya Litinin cewa, ya zuwa yanzu, cutar COVID-19 ba ta kawo babbar illa ga nahiyar Afrika ba, wato cutar ba ta samu barkewa sosai a nahiyar ba.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana ta bidiyo, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, ko da yake cutar ta bulla cikin unguwanni a rabin kasashen Afrika, alkaluman da WHO ta bayar kan yawan mutanen da suka kamu da cutar na nuna cewa, ya zuwa yanzu, cutar ba ta kawo babbar illa ga nahiyar ba. Yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai kashi 1.5% bisa na dukkan wadanda suka harbu da cutar, sannan yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ya kai kasa da kashi 0.1% bisa na duk adadin a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China