Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya na ganin cewa wasikar Donald Trump ta illata WHO
2020-05-21 11:21:48        cri

Jiya Laraba, babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, ya samu wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aiko masa, yana kuma nazarin abubuwan da ya rubuta. A cewasa, kudaden da WHO ke kashewa a kowa ce shekara bai wuce dala biliyan 2.3 ba, kwatankwacin kudin da aka kashe a shekara a wani matsakaicin asibitin a kasashe masu wadata, amma ayyukan da WHO take gudanarwa ya shafi duk fadin duniya.

Ya kara da cewa, WHO ta kaddamar asusu neman taimako kudade a shekarar 2018, ta yadda za a kara taimakawa wasukasashe masu bukata da kudade. Ya nanata cewa, tun bayan da ya hau wannan mukamin ababban sakataren WHO, yana kokarin aiwatar da wannan aiki, don warware matsalar kudade da aka fuskanta

A wannan rana, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Mousavi ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, wasikar da Donald Trump ya aikawa WHO ta illata kungiyar matuka, saboda WHO hukuma ce mai zaman kanta da kuma take aiwatar da ayyuka masu muhimmanci. Don haka bai kamata Trump yayi haka a wannan lokaci ba ko kadan.

Bayanai na cewa, a wannan rana, mataimakiyar farfesa a kwalejin doka da shari'a na jami'ar Warwick ta kasar Birtaniya, Madam Sharifa ta shedawa manema labarai cewa, ita da abokan aikinta , sun girgiza matuka da abubuwan dake cikin wasikar Donald Trump, wanda bai fahimci yadda WHO da kuma sauran kasashe na tunkarar matsaloli ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China