Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta sanar da kafa asusu don magance kalubalolin kiwo lafiya
2020-05-28 13:32:35        cri

Jiya Laraba, a gun taron manema labarai ta kafar bidiyo, babban jami'in hukumar lafiya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar da kafa asusun hukumar, don tattara kudi, ta yadda za a magance kalubalolin kiwon lafiya a fadin duniya cikin gaggawa. A cewarsa, kafuwar asusun wani muhimmin mataki ne a tarihin WHO.

Wannan asusu mai hedkwata a birnin Geneva zai biya bukatun kiwon lafiya na kasa da kasa ta hanyar samarwa wasu hukumomi da kungiyoyi kudade ciki har da WHO, da zummar amfanawa karin jama'ar duniya da yawansa ya kai biliyan 1, da kiyaye karin mutane a halin gaggawa da yawansa ya kai biliyan 1, da kuma kyautata zaman rayuwa da lafiyar karin mutane da yawansa ya kai biliyan 1. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China