Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Gudummawar jini wani makami ne na karfafa matakan yaki da COVID-19
2020-06-15 10:03:24        cri
Darektar hukumar lafiya ta duniya mai kula da shiyyar Afirka Matshidiso Moeti, ta bayyana cewa, wajibi ne kasashen duniya su kara zuba jari wajen samar da kayayyakin more rayuwa su kuma ilimantar da jama'a, kan yadda za su kara ba da gudummawar jini mai tsafta da ma karfafa matakan yaki da cutar COVID-19.

Babbar jami'ar ta bayyana haka ne, yayin bikin ranar gudummwar jini ta duniya da aka gudanar jiya Lahadi. Tana mai cewa, ya kamata gwamnatoci su bullo da matakan da za su kwataidar da jama'a kara ba da gudummawar jini mai tsafta, yayin da ake fama da karancinsa a gabar da ake yaki da annobar COVID-19.

Moeti ta ce, a lokacin da ake yaki da wannan annoba, samar da jini abu ne mai hadarin gaske. Wannan ne ma ya sa aka dakatar da ba da gudummawar jinin, kana dokar kulle da aka sanya, da fargabar kamuwa da cutar, sun hana jama'a ba da gudummawar jinin da suka saba yi a baya.

A cewar jami'ar ta WHO, tuni ma katse hanyoyin ba da jinin dake da nasaba da cutar, ya haddasa karancin kayayyakin da ake bukata na ba da gudummawar jinin da ma karawa masu bukata.

A don haka, ta ce amfani da dan tayin jini daga marasa lafiyan da suke warke daga cutar COVID-19, don rage kaifin cutar ga wadanda suka harbu, ya sake nanata bukatar kasashe su rika samun isasshen jini da ake bukata.

Ta kuma yaba kokarin kasashen na Afirka, na ba da gudummawar jini, a wani mataki na amfani da dan tayin jini don warkar da COVID-19, yayin da yawan wadanda ke kamuwa da cutar ke karuwa a nahiyar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China