Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu ta karbi kaso na uku na tallafin kayayyakin lafiya daga gidauniyar Jack Ma
2020-06-02 09:34:55        cri
Kasar Sudan ta kudu ta karbi kashi na uku na gudunmowar kayayyakin kiwon lafiya daga gidauniyar Jack Ma da Alibaba domin yaki da cutar COVID-19.

Hua Ning, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu ya ce, kashi na uku na kayayyakin tallafin da gidauniyar ta baiwa Afrika sun hada da takunkumin rufe baki da hanci miliyan 4.6, da kayayyakin gwaje-gwaje 500,000, na'urar taimakawa numfashi 300, da rigunan bada kariya 200,000, gilasan kare fuska 200,000, da na'urar gwajin yanayi 2,000, da na'urar auna zafin jiki 100, sai safar hannu 500,000.

Cikin sanarwar da ya fitar a Juba, mista Ning ya ce, ya yi matukar farin ciki ganin cewa Sudan ta kudu ta karbi kaso na uku na kayayyakin tallafin kiwon lafiyar daga Ma Yun, wato gidauniyar Jack Ma da Alibaba.

Jakadan na Sin ya ce, tallafi na baya bayan nan da aka baiwa kasar ta Afrika mafi yarinta kungiyar tarayyar Afrika ce ta rarraba su.

Kawo yanzu, Sudan ta kudu tana da adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 kimanin 994, yayin da mutane 6 sun warke, sai mutane 10 da suka mutu a duk kasar ya zuwa ranar 27 ga watan Mayu.

An samu karuwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar ne bayan da gwamnati ta sassauta dokar hada fita a ranar 25 ga watan Mayu a matsayin wani mataki da zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar ta COVID-19 a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China