Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkawarin da Sin take yi game da yakar COVID 19 ya samu yabowa daga bangarori daban-daban a duniya
2020-05-21 11:09:27        cri

Jiya Laraba, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna cewa, an samu ci gaba a babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 73 da ya gudana, matakin da ya bayyana hadin gwiwar kasa da kasa da ba a taba gani ba, yana mai godiya ga mambobin kasashe da suka zartas da kudurin yakar COVID-19 a duniya.

Kuduri ya tsai da taswira mai inganci ta fuskar daukar muhimman matakan yakar cutar, da kuma rarraba nauyi a tsakanin mambobin WHO, don kiyaye da kuma ingiza kasashen duniya daukar matakan da suka dace a wannan fanni.

Rahotanni na cewa, a yayin taro na ran 18 ga wata, shugaban kasar Sin ya sanar da muhimman matakai 5 da suka dauka don ingiza hadin kan kasa da kasa ta fuskar yakar cutar, tare da yin kira ga kasashen duniya da su hada kai don raya al'umma ta bai daya a fannin kiwo lafiyar Bil Adama, matakin da ya samu yabowa daga bangarorin daban-daban.

Kafar yada labarai ta POLITICO ta Amurka ta ba da labari cewa, ko da yake Donald Trump ya rage taimakon da Amurka ke baiwa WHO, amma kasar Sin ta ci gaba da hada kai da WHO don taka rawa wajen yakar cutar a duniya gaba daya.

Ya zuwa yanzu, ana nuna damuwa kan hadin kai wajen yakar cutar da kuma samar da sabuwar allurar rigakafi. Sin ta sanar da cewa, Sin za ta samar da allurar ga duk fadin duniya da zarar ta kirkiro ta da yin amfani da ita, don ba da gudunmawarta wajen samar da allurar ga kasashe masu tasowa.

Shafin yanar gizo na gidan telibijin na France 24 ya ba da labari cewa, sanarwar kasar Sin ta zo a daidai lokacin da kasa da kasa suke kokarin yin takara domin fito da wani sabon maganin yakar cutar, abin da Sin take so shi ne baiwa sauran kasashe taimako da tallafin jiyya. Ya zuwa yanzu, Sin tana bincike kan allura nau'o'i 5, kuma tana kokarin fito da sabbin alluran riga kafi da dama.

Shafin yanar gizo na Business Insider na Amurka ya ba da labari cewa, a gun taro na WHO, Sin ta sanar da tsarin hadin kai na kafa asibitoci 30 don tallafawa Afrika, da gaggauta raya hedkwatar cibiyar kandagarkin cututuka ta Afrika, don taimakawa wajen kara karfin kandagarkin cututuka a nahiyar. Matakan da Sin take dauka a duniya sun bayyana mutuncin kasar Sin. Babu shakka, Sin na nuna karfinta na ba da jagoranci a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China