Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Sin da Faransa na hadin kan daukar sinima "Halittu masu kwaikwayon dabi'un dan Adam na Peking: asirin karshe na 'yan Adam"
2020-06-14 16:56:12        cri

 

Ranar 13 ga wata, rana ce ta kare al'adun gargajiya da muhalli mai ni'ima wadanda aka gada daga kaka da kakanni, inda aka kaddamar da biki ta yanar gizo game da soma aikin daukar shirin sinimar bincike mai taken "Halittu masu kwaikwayon dabi'un 'yan Adam na Peking: asirin karshe na 'yan Adam" bisa hadin gwiwar kasashen Sin da Faransa a biranen Beijing da Paris. Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al'umma na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban CMG Shen Haixiong, da ministan al'adun kasar Faransa Franck Riester sun sanar da soma aikin tare.

Bisa ga shirin da aka tsara, za a maida shirin sinimar a matsayin wani aiki ne na bikin shekarar yawon shakatawar al'adu na kasashen Sin da Faransa, kuma za a watsa a watan Disamba na shekarar 2021.

 

 

Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana a yayin jawabinsa cewa, shirin sinimar ya yi bayani kan yin mu'amalar al'adu, da jaddada kafa dandalin hadin kai tare da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai, hakan ya dace da yanayin da ake ciki.

A nasa bangaren, ministan al'adun kasar Faransa Franck Riester ya bayyana cewa, "Irin ayyukan hadin kai sun ba mu damar fahimtar yadda 'yan Adam suke yin mu'amala a cikin shekaru aru-aru da suka gabata, tushen alakar dake tsakanin kasashen Faransa da Sin imanin bai daya ne namu."

Wadanda suka halarci bikin sun hada da babbar daraktan kungiyar UNESCO ta MDD Audrey Azoulay, jakadan kasar Faransa dake kasar Sin Laurent Bili, mamba taron edita na CMG Xue Jijun da kwararru da masana na kasashen biyu da kuma muhimman ma'aikata masu shiga aikin sinima. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China