Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karon farko CMG ya yi amfani da fasahar sadarwar "5G+8K" domin gabatar da shirye-shirye
2020-05-20 17:00:30        cri

Domin shirye-shiryen taruka biyu na kasar Sin a bana, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya yi amfani da fasahar sadarwar zamani ta "5G+8K" domin turawa gami da tsara shirye-shirye, wanda ya zama karon farko a kasar.

Jiya Talata, CMG ya shirya bikin kaddamar da makon tallata fasahar sadarwar zamani ta "5G+4K/8K+AI" a Beijing, inda mataimakin shugaban sashin fadakar da al'umma na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG Shen Haixiong, da sauran wasu manyan jami'ai na CMG da na kamfanonin ChinaMobile, da ChinaTelecom, da kuma ChinaUnicom suka halarci bikin.

Mista Shen Haixiong ya bayyana cewa, a bana, CMG zai nuna himma da kwazo wajen zama wata muhimmiyar kafar yada labarai mai taka rawa daga dukkan fannoni a duniya, da kara gabatar da shirye-shirye ta hanyoyi daban-daban, musamman bisa fasahar sadarwar zamani ta "5G+4K/8K+AI".(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China