Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG yana gabatar da cikakkun bayanai kan yaki da cutar numfashi
2020-02-16 20:50:11        cri

Tun bayan barkewar cutar numfashi, sai kamfanin dillancin labaran bidiyon kasa da kasa na gidan talibijin na kasar Sin wato CCTV dake karkashin jagorancin babban rukunin gidajen radiyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya fara gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsa da sauran kafofin watsa labaran kasashen duniya, inda ya gabatar da cikakkun bayanai kan yadda ake kokarin yaki da cutar ba dare ba rana ta hanyoyi daban daban da kuma ta harsuna daban daban, haka kuma ya yi bayani kan ci gaban da aka samu a bangaren ta hanyar samar da hakikanin abubuwan da suka faru a fadin kasar a ko da yaushe.

Ya zuwa yau ranar 16, kafofin watsa labaran kasa da kasa da yawansu ya kai 80 wadanda suka hada da Reuters da BBC da AP da AFP da ABU da EBU da ASBU da kawancen kafofin watsa labaran Latin Amurka da sauran kafofin watsa labaran shiyya shiyya guda biyar sun taba aikawa CMG sakonni, inda suka yaba da namijin kokarin da ya yi domin samar musu labaran da dumi dumi kan hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, da matakan da ta dauka yayin da take kokarin dakile yaduwar cutar.

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, tun daga ranar 21 ga watan Janairun bana, a kowace rana kusan gidajen talibijin 1284 na kasashe da yankuna 77 suna gabatar da labaran da CMG ya samar musu wadanda suke shafar matakan shawo kan yaduwar cutar da gwamnatin kasar Sin ta dauka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China