Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An Kaddamar Da Bikin Nuna Kayayyakin Tarihi Ta Kafofin Watsa Labaru A Biranen Beijing Da Guilin
2020-06-13 20:19:40        cri

A yau Asabar, an gudanar da bikin nuna kayayyakin tarihi ta kafofin watsa labaru a birnin Beijing da Guilin, wanda biki ne da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin, suka gudanar tare. Inda shugaban kamfanin CMG, mista Shen Haixiong, da datektan hukumar kula da kayayyakin tarihin mista Liu Yuzhu suka halarta.

An ce kamfanin CMG da hukumar kare kayayyakin tarihi za su yi hadin gwiwa, wajen nuna wasu al'adun gargajiya, da kayayyakin da aka gada daga kaka da kakanni, da yadda ake kokarin kare kayayyakin tarhi a kasar Sin, ta hanyar wasu sabbin dabarun watsa labaru, cikin watanni 3 masu zuwa. Ta wannan aiki ana neman baiwa jama'a damar kara fahimtar muhimmancin kayayyakin tarihi, da al'adun da suka nuna. Ban da wannan kuma, ana neman janyo hankalin karin matasa, domin su ma su taka rawar gani a kokarin mika al'adun gargajiya daga zuriya zuwa wata. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China