Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun gabatar da wasu sharhin da CMG ya gabatar game da jita-jitar yan siyasar Amurka
2020-05-16 20:27:22        cri

A kwanakin baya, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da wasu sharhi a jere kamar su "Pompeo Dan Siyasa Ne Maras Dattaku", da "Laifuka Guda 4 Da Mike Pompeo Ya Aikata", da "Mike Pompeo Ya Kara Fitar Da Jita-jita A Gaban Kimiyya" da sauransu, inda suka zargi 'yan siyasar kasar Amurka masu nuna kiyayya ga kasar Sin da kara gabatar da jita-jita game da Sin, don kaucewa sauke nauyinsu na yaki da cutar COVID-19, da ceton kuri'un goyon bayan daga jama'a. Sharhin sun jaddada cewa, kamata ya yi 'yan siyasar kasar Amurka sun dauki alhakin yaduwar cutar COVID-19 a duniya, kana kasa da kasa su yi bincike kan ayyukan yaki da cutar COVID-19 na kasar Amurka.

Shirin gabatar da labarai, kamfanin dillancin labaru ta bidiyo na kasa da kasa, kafar CGTN da ma sauran shirye-shirye na gidan CMG sun gabatar da sharhin a jere da Turanci da kuma sauran harsuna, lamarin da ya ja hankalin kasa da kasa sosai. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa fiye da 100 ciki har da kafar CNN ta kasar Amurka, da kamfanin BBC na kasar Birtaniya, da gidan telebijin na 24 na kasar Faransa, da jaridar Wall Street da mujallar Newsweek na kasar Amurka, da jaridar The Times ta kasar Birtaniya, da kamfanin AFP na kasar Faransa da sauransu sun tsamo sharhin CMG. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China