Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Siyasan Kasar Amurka Sun Fara Dora Laifi Ga 'Yan Asalin Kasashen Latin Amurka
2020-06-13 20:44:18        cri

"Za a tilasta Mexico daukar alhakin barkewar sabon zagayen annoba a kasar Amurka?" Cikin wani bayanin da jaridar El Financiero ta kasar Mexico ta watsa a kwanakin baya, ta shafin yanar gizo na Intanet, an rubuta wadannan kalmomi, don nuna matukar takaici kan yadda wasu manyan jami'an kasar Amurka suka dora alhakin lalacewar yanayin cutar COVID-19 a kasarsu ga mutane masu yawon shakatawa na kasar Mexico.

Dalilin da ya sa 'yan siyasan kasar Amurka ke neman dora wa kasar Mexico laifi, shi ne domin yawancin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kwanakin baya, suna zama ne a ungwannin da aka fi samun 'yan asalin kasashen Latin Amurka, lamarin da ya sanya 'yan siyasan ke cewa, an shigo da cutar ne daga kasar Mexico a wannan karo. Ko da yake tushen wannan dalilin ba shi da karfi.

Hakika bayan samun barkewar annobar a kasar Amurka, mutane 'yan asalin kasashen Latin Amurka sun fi jin radadin cutar, inda da yawa daga cikinsu suka kamu da cutar, wasu har ma suka rasa rayuka. Batun nan ya nuna yadda ake samun rashin daidaito tsakanin kabilun kasar Amurka. Sa'an nan, kamar yadda aka rubuta a cikin wani sharhin da jaridar New York Times ta watsa, dalilin da ya sa ake samun gibi tsakanin lafiyar 'yan asalin kasashen Afirka, da na Latin Amurka, da sauran al'umomin kasar Amurka, shi ne, ba a taba samun wani daidaito ba a tarihin kasar tsakanin wadannan al'ummomi, a fannonin kudin shiga da damar raya kai.

Ta wannan za mu iya ganin cewa, yadda ake nuna hakuri ga kabilanci ya haddasa sauran matsaloli masu alaka da rashin daidaito tsakanin al'ummomi, amma su 'yan siyasan kasar Amurka sun yi biris da haka, yayin da suke kokarin neman dora laifi ga wadanda suke ta shan wahala sakamakon manufarsu ta nuna bambanci.

Kamata ya yi mu tunatar da 'yan siyasan kasar Amurka cewa, kar su manta da ma'anar kalmar "adalci", yayin da suke kokarin dora laifi ga sauran mutane. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China