Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko kamfanonin Amurka za su bar kasar Sin?
2020-06-05 13:46:58        cri

Jaridar Wall Street ta kasar Amurka ta gabatar da wata tambaya a kwanan baya cewa, shin Amurka tana shirin katse huldarta da kasar Sin ne? Inda ta yi gargadi da cewa, ya kamata masu ra'ayin fadada tasirinsu a fannin tsaron Amurka su fahimci cewa, katse huldar da ke tsakanin kasashen biyu a fannin samar da kayayyaki da ba da ilmi, zai illata karfin takara na Amurka matuka.

Wall Street ta wallafa wannan bayani ne, ganin yadda wasu 'yan siyasar Amurka ba su mai da hankali kan bude kofar yin hadin gwiwa don kara samun taimako a halin da ake ciki na tsaka da fama da tasirin cutar COVID-19, a maimakon haka, suna ikirari katse huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da kawar da tasirin kasar Sin a fannin masana'antu bisa tunanin ra'ayin yakin cacar baki da bangaranci, ta yadda tilas wani bangare na daban ya yi hasara. Alal misali, mashawarcin tattalin arziki na White House Lawrence Alan Kudlow ya zuga kamfanonin Amurka da su fice daga kasar Sin sun koma Amurka. Wasu 'yan siyasa kuma sun yi shawarar kaddamar da asusun dala biliyan 25 , domin dawo da kamfanoni, inda suka yi ikirarin cewa, zamanin samar da guraben aiki a ketare ya kare.

A hakika, kamfanonin Amurka da dama ba su amince da shawarar 'yan siyasa irinsu Lawrence Alan Kudlow ba ko kadan. Kwanan baya, kamfanin Honeywell na Amurka ya kafa hedkwatar kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa kana cibiyar kirkire-kirkire a birnin Wuhan, haka kuma kamfanin Tesla ya sanar da kara yawan motocin da yake samarwa a birnin Shanghai, yayin da kamfanin Exxon Mobil ya fara wani sabon shirinsa a lardin Guangdong, haka zalika kamfanin Costco na shirin bude reshensa na biyu a Shanghai, ban da wannan kuma kamfanin Starbucks ya sanar da kafa wata cibiyar kirkire-kikire a kasar Sin. Babban darektan kungiyar 'yan kasuwan Amurkawa dake kasar Sin Alan Beebe ya ce, bayan Sin ta cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, tana sahun gaba a duniya wajen farfado da tattalin arziki. Dalilin da ya sa kamfanonin da suka yanke shawarar kafa rassansu a kasar Sin a baya, haka ma lamarin ma yake yauzu.

Abu mai jawo hankali shi ne, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da daftarin raya tashar ciniki cikin 'yanci na tsibirin Hainan, wanda kuma ya kawar da harajin wasu kayayyaki da za a biya, da gabatar da gatancin harajin da za a biya da shigo da masu hazaka da kwarewa da kuma takaita tsarin kwastan da sassauta aikin ba da izni da kuma ba da hidimomi tsakanin kasa da kasa da bude kofa ga sana'ar hada-hadar kudi da dai sauransu. Abin da ya bayyana cewa, Sin tana kokarin daukar matakai da suka dace don kara bude kofa ga ketare da ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, babu shakka wannan mataki, zai kara karfin kasuwannin kasar Sin na jawo hankalin kasa da kasa da kuma baiwa kasashen duniya zarafi mai kyau na samun bunkasuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Ko akwai 'yancin bayyana ra'ayi a Amurka? 2020-06-03 20:28:36

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China