Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu wanda zai iya mayar da hannun agogo baya
2020-06-05 17:13:42        cri

A kwanan nan, gwamnatin Amurka ta saba alkawarin da ta yi, wato ta bada umarnin kafa shinge ga dalibai gami da manazartan kasar Sin wadanda za su je karatu ko aiki a Amurka, bisa hujjar cewa, wai dalibai da manazartan Sin za su yiwa Amurka leken asiri da sauran wasu ayyukan da suka shafi tsaro. Amma masu iya magana na cewa, zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya.

Babu tantama, irin wannan abun da Amurka ta yi, cin zarafi ne gami da nuna wariyar launin fata ga Sinawa, al'amarin da ya keta hakkin dalibai da manazartan kasar Sin, baya ga yin mummunan tasiri ga mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Amurka.

 

Zargin da aka yiwa dalibai da manazartan kasar Sin ba shi da tushe balle makama. Rahotanni da jaridar New York Times ta wallafa na cewa, wasu jami'an gwamnatin Amurka na ganin cewa, babu shaidu dake nuna cewa wadannan daliban kasar Sin da ba za su samu izinin shiga Amurka wato viza ba, sun aikata wani abun da bai dace ba. Haka kuma jami'o'i daban-daban na Amurka sun soki wannan kudurin da gwamnatin kasar ta dauka. Alal misali, wani babban jami'i daga jami'ar Harvard ya ce bai gane abin da Amurka ke nufi da kalmar "leken asirin ilimi" ba, inda a cewarsa, makasudin nazarin ilimi shi ne wallafa sakamakon nazari sa'annan a raba shi ga duk duniya. Shi ma shugaban jami'ar Columbia ya jaddada kin amincewarsa ga bukatar hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka wato FBI ta sa ido kan daliban da aka haife su a kasashen waje, musamman dalibai da manazarta 'yan asalin kasar Sin.

Idan mun dubi tarihin ci gaban dangantakar Sin da Amurka a cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, mu'amalar al'adu ciki har da na ilimi tsakanin kasashen biyu sun samu goyon-bayan bangarori daban-daban. Yanzu adadin daliban kasar Sin da suke karatu a Amurka ya zarce dubu 400, amma duk da cewa Amurka ta sha yin alkawarin cewa, wai tana maraba da zuwan daliban kasar Sin, amma gaskiyar magana ita ce, tana yunkurin kawo cikas ga tsarin mu'amalar dalibai da ilimi tsakanin kasashen biyu.

Mutane da dama a Amurka sun bayyana cewa, ci gaba da yin ja-in-ja tsakanin Sin da Amurka zai kawo babbar illa ga Amurka. Kamar a wannan karo, bayan da gwamnati ta bada umarnin sanya haramci kan dalibai da manazartan kasar Sin, akwai jami'o'i da kwalejoji da yawa a Amurka, wadanda suka bayyana rashin jin dadinsu, inda suka ce, hakan zai illata ci gaban harkokin nazarin kimiyya da fasaha, da illata tsarin al'adu da tabarbarewar harkokin kudi a makarantu。

Sin da Amurka, manyan kasashe biyu ne dake taka muhimmiyar rawa a harkoki na duniya, kuma kara kyautata dangantakar kut da kut tsakaninsu ya dace da muradun kasashen. Muna kira ga Amurka ta gyara kuskuren da ta aikata, da yin watsi da ra'ayinta na nuna wariyar launin fata, da dakatar da kawo cikas ko matsa lamba ga dalibai da manazartan kasar Sin ba tare da bata lokaci ba. Gyara kayanka, aka ce bai zama sauke mu raba ba. Sanin kowa ne cewa, babu wanda zai iya mayar da hannun agogo baya, kuma kara saukaka ayyukan sada zumunta tsakanin al'ummar Sin da Amurka, ya dace da hakikanin halin da ake ciki da ma muradunsu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China