Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bukukuwan ranar kare aladun gargajiya da muhalli a kasar Sin
2020-06-13 16:12:52        cri

Yau Asabar rana ce da MDD ta kebe domin jaddada muhimmancin kare al'adun gargajiya, da muhalli mai ni'ima, wadanda aka gada daga kaka da kakani. Don wannan rana ta musamman, ana gudanar da wasu bukukuwa fiye da 4,600 a wurare daban daban na kasar Sin, da nufin nuna kwarin gwiwar mutanen kasar kan al'adunsu na gargajiya, da amfani da al'adu wajen raya kauyuka, da taimakawa aikin kawar da talauci.

A birnin Guilin dake kudancin kasar Sin, an shirya gagarumin biki na tunawa da ranar, inda darektan hukuma mai kula da aikin kare kayayyakin tarihi ta kasar Sin, Mista Liu Yuzhu, ya ce yawan wurare ko kuma gine-gine masu tarihi na kasar Sin ya kai dubu 767, yayin da yawan kayayyakin tarihin da aka adana ya kai miliyan 108. Ta ce a shekarun baya, kasar ta dauki jerin matakai don kare kayayyakin tarihi, gami da taimakawa karewa da kuma gadon al'adun gargajiya.

Babban jigon bukukuwan wannan shekara shi ne " kare kayayyakin tarihi, gami da kokarin wanzar da zaman walwala", inda aka fi mai da hankali kan amfani da al'aun gargajiya wajen samar da guraben aikin yi ga jama'a, ta yadda za a samu ci gaba a aikin kawar da talauci a kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China