Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da EU sun tattauna batun kyautata dangantaka yayin taron koli karo na 10
2020-06-10 11:55:29        cri

Yayin taron kolin da suka gudanar karo na 10 a ranar Talata, Sin da Kungiyar Tarayyar Turai EU, sun amince za su karfafa alakar dake tsakaninsu kan wasu muhimman batutuwa.

Tattaunawar, wacce ta gudana ta kafar bidiyo, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, shi ne ya jagoranta tare da Josep Borrell, babban wakilin harkokin kasashen waje da tsaro na EU.

Wang ya ce, batun yin hadin gwiwa da cimma daidaito a koda yaushe sune mafi muhimmanci maimakon yin gasa da nuna banbance banbance, dangantakar Sin da EU dadaddiya ce, cikakkiya ce, kuma muhimmiya ce ga bangarorin biyu. Wang ya kara da cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su gudanar da bikin cika shekaru 45 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakaninsu yayin da suke shiga sabon zagaye na bunkasuwar dangantakar dake tsakaninsu.

Ya bukaci bangarorin biyu su kara ingiza matsayin dangantakar dake tsakaninsu bayan kawar da annobar COVID-19, kuma su kara karfafa matsayin cudanyar dake tsakaninsu, kana su yi kyakkyawan shirin gudanar da taron kolin Sin da EU da taron shugabannin Sin da EU.

A nasa bangaren, Borrell ya ce, EU tana da kyakkyawan tsammanin game da dangantakar dake tsakaninta da Sin kana za ta dauki dukkan matakan karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. Dukkan bangarorin biyu EU da Sin masu taimakawa juna ne game da bunkasuwar cudanyar bangarori daban daban, ya ce, EU tana maraba da kuzarin da kasar Sin ke nunawa a harkokin hadin gwiwar kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China