2019-09-21 16:48:29 cri |
Shugaba Nkurunziza ya ce, cikin shekaru 56 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Burundi da Sin, sun raya dangantakar dake tsakaninsu, kana Sin ta zama abokiyar hadin gwiwa ta musamman ta kasar Burundi a duniya.
Ministan kula da albarkatun ruwa da makamashi da ma'adinai na kasar Burundi ya bayyanawa 'yan jarida cewa, yawan wutar lantarki da tashar samar da wutar lantarkin za ta samar ya kai mafi yawa bisa adadin wutar lantarki da aka samar a dukkan kasar, wadda kuma ke da muhimmanci sosai wajen raya kasar a nan gaba.
Jakadan Sin dake kasar Burundi Li Changlin ya bayyana cewa, ban da tashar samar da wutar lantarki, Sin tana gudanar da ayyukan bada taimako a fannonin aikin noma, da bada ilmi, da kiwon lafiya da sauransu a kasar Burundi. Ya ce yanzu an shiga lokaci mafi kyau na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Burundi, kuma bisa yanayin da ake ciki a kasar Burundi, Sin za ta kara taimakawa kasar Burundi kara karfinta a nan gaba. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China