Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar Sin ta fitar da makala da ta bayyana yanayin da batun kare hakkin bil Adama ke ciki a Amurka
2020-06-11 11:16:41        cri
Cibiyar nazarin harkokin kare hakkin bil Adama ta kasar Sin, ta fitar da wata makala da ta fayyace yanayin da ake ciki game da batun kare hakkin bil Adama a Amurka.

Makalar mai taken "Cutar COVID-19 ta sake fayyace ainihin yanayin kare hakkin bil Adama a Amurka", ta bankado akidun gwamnatin kasar na son kai, da karancin hangen nesa, da gazawa, da rashin sanin ya kamata yayin da take tunkarar cutar, akidun da su ne suka jefa Amurkawa kusan miliyan 2 cikin hadarin kamuwa da cutar, yayin da wasu kuma sama da 110,000 suka rasa rayukan su.

Makalar ta kara da cewa, yanayin da ake ciki, ya kara fito da dadaddun matsaloli, wadanda a yanzu ke kara ta'azzara a Amurka, kamar rarrabuwar kan al'ummun kasar, da wagegen gibin dake tsakanin talakawa da mawadata, da wariyar launin fata, da karancin kariya ga moriyar al'umma da sauran marasa galihu. Hakan a cewar makalar ya jefa Amurka da dama cikin matsanancin kalubalen keta hurumin su.

Bugu da kari, cikin makalar an yi nuni da yadda gwamnatin Amurka, ta yi watsi da gargadin da aka yi mata game da cutar, maimakon haka ta mayar da hankali ga kare moriyar jari hujja, tare da siyasantar da ayyukan kawar da cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China