Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira ga Canada da ta gaggauta sakin Meng Wanzhou
2020-05-27 10:58:29        cri

A jiya Talata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya kara jan hankalin mahukuntan kasar Canada, da su gyara kuskuren da suka yi, su kuma gaggauta sakin jami'ar kamfanin Huawei Meng Wanzhou, tare da tabbatar da dawowar ta Sin lami lafiya.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake amsa tambayar wani dan jarida, game da shirin wata kotun kasar Canada na yanke hukunci, game da tsare Meng Wanzhou da ake ci gaba da yi.

Jami'in ya ce matsayar Sin game da wannan batu a fili take, cewa Amurka da Canada sun keta hurumin yarjejeniyar kasa da kasa ta tusa-kyarar wanda ake zargi, sun kuma kera martabar 'yar asalin kasar Sin ba tare da bin wata ka'ida ba. Zhao ya kara da cewa, wannan lamari ne na siyasa da ya yi matukar keta 'yanci, da mutuncin 'yar kasar Sin.

Bugu da kari, jami'in ya ce gwamnatin Sin za ta ci gaba da daukar dukkanin matakan da suka wajaba na kare hurumi, da 'yancin Sinawa. A daya bangaren kuma, Sin na fatan Canada za ta gyara kuskuren ta, ta saki Meng, da ba ta damar dawowa gida cikin sauri, domin kaucewa kara gurgunta alakar sassan biyu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China