Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhao Lijian: kudurin dokar Amurka mai nasaba da Xinjiang na nuni ga bakar aniya da baki biyu
2020-05-29 21:38:02        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce matakin tattaunawa, tare da zartas da kudurin dokar kare hakkin dan Adam, mai nasaba da yankin Xinjiang na al'ummar Uyghur da majalissar wakilan Amurka ta dauka, na nuni ga bakar aniya, da baki biyu da 'yan siyasar Amurka ke nunawa a zahiri.

Zhao Lijian ya bayyana hakan ne a yau Juma'a a nan birnin Beijing, yana mai cewa matakin na Amurka, ya bayyana baki biyu da kasar ke yi game da batun yaki da ta'addanci, da mugun nufin kasar ta hanyar tsoma baki cikin harkokin wajen kasar Sin.

Jami'in ya ce ta hanyar fakewa da dokokin majalissar ta Amurka, kasar na zargin Sin da keta hurumin 'yancin bil Adama a Xinjiang, da sukar manufofin Sin na gudanar da mulkin yankunanta, da muzanta kokarin Sin na yaki da tsattsauran ra'ayi da yanayi mai tsanani, ta yadda Amurkan ta kai ga tsoma baki cikin harkokin gidan Sin.

Ya ce Sin na bayyana matukar rashin gamsuwa, da Allah wadai da wannan mataki na Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China