Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta samar da goyon-baya ga jama'ar kasashe daban-daban ciki har da Amurka don yakar cutar COVID-19
2020-05-07 20:37:01        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis cewa, kasarta za ta ci gaba da iyakacin kokarinta, wajen samar da goyon-baya, da taimako ga jama'ar kasashe daban-daban, ciki har da na Amurka, domin dakile yaduwar annobar numfashi ta COVID-19.

A 'yan kwanakin nan, kungiyar sada zumunta da jama'ar kasashen waje ta jihar Guangxi, ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta samar da kyautar wasu kayayyakin yakar annobar COVID-19 ga kwamitin FTHO ta kasar Amurka, ciki har da abubuwan rufe baki da hanci na aikin likita 6000, da safar hannu ta aikin likita 4000, kuma kwamitin ya riga ya samu wadannan kayayyakin. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China