Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi kira da a zurfafa bincike game da yadda wadanda ba sa nuna alamar harbuwa da COVID-19 ke iya yada cutar
2020-06-11 09:33:38        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce akwai bukatar zurfafa bincike game da yadda wadanda ba sa nuna alamar harbuwa da COVID-19 ke iya yada cutar bayan sun kamu da ita.

Mr. Tedros wanda ya bayyana hakan, yayin ganawa da manema labarai ta kafar bidiyo daga birnin Geneva a jiya Laraba, ya ce akwai bukatar kara bincikar dalilan da suke sawa, masu dauke da COVID-19 da ba sa nuna alamar harbuwa da ita, ke iya ci gaba da yada ta ga masu lafiya.

Ya ce "Tun a farkon watan Fabarairu, aka lura da wannan yanayi, don haka akwai bukatar zurfafa bincike. Kuma duk da yake an fahimci wasu muhimman abubuwa game da cutar, kawo yanzu ana ci gaba da nazarin ta, domin samun karin haske bisa abubuwa da dama da suka shigewa masana kiwon lafiya duhu.

Tedros ya kara da cewa, hukumar WHO za ta ci gaba da fitar da shawarwari ga al'ummar duniya game da cutar ba tare da wani jinkiri ba. Daga nan sai ya jaddada muhimmancin kebe masu dauke da cutar, da gwada wadanda suka nuna alamun ta, tare da bincikowa, da kebe wadanda suka yi cudanya da su, a matsayin hanyoyi mafiya inganci, na dakile kara bazuwar cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China