Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi kira da mayar da hankali kan al'umma yayin da ake saukaka matakan yaki da COVID-19
2020-05-29 12:48:25        cri
Ofishin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO a Turai, ya yi kira da mayar da hankali kan al'umma yayin da ake kokarin farfado da tattalin arziki, bisa la'akari da yadda tattalin arzikin ke tafiya kafada-da-kafada da matakan yaki da COVID-19.

Daraktan ofishin Dr. Hans Kluge ya bayyana yayin da taro ta kafar bidiyo da aka saba yi cewa, babu batun tattalin arziki idan ba mutane. Don haka ba yadda za a iya farfado da tattalin arziki ba tare da an takaita yaduwar cutar ba.

Ya ce bangaren kiwon lafiyar al'umma ne zai ingiza irin wannan kokari na farfado da tattalin arziki, kuma bisa sanya al'ummar a gaba da komai.

Ya kara da cewa, wajibi ne irin wannan tattalin arziki ya zama mai bada gudunmuwa ga kiyaye muhalli da yanayi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China