Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tura rukunin kwararrun likitoci zuwa Equatorial Guinea don yakar COVID-19
2020-05-26 19:42:05        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau talata cewa, gwamnatin kasar ta tura wani rukunin kwararrun likitoci zuwa kasar Equatorial Guinea don taimaka mata yakar cutar numfashi ta COVID-19. Tawagar likitocin da ta isa birnin Malabo a jiya Litinin, za su yi musanyar ra'ayoyi da jami'an ma'aikatar lafiya, da na kwamitin dakilewa gami da sa ido kan kwayar cutar COVID-19 na Equatorial Guinea, gami da ma'aikatan sakatariyar hukumar WHO dake kasar. Har wa yau, likitocin Sin za su ziyarci asibitocin kula da masu kamuwa da cutar, gami da dakunan gwaje-gwaje dake birnin Malabo, domin samar da horo kan dabarun yakar cutar.

Game da wannan batu, Mista Zhao ya bayyana cewa, tura kwararrun likitoci zuwa Equatorial Guinea da kasar Sin ta yi, ya tabbatar da akidun dake tattare da muhimmin jawabi da shugaba Xi Jinping ya gabatar a wajen bikin bude babban taro kan harkokin lafiya na kasa da kasa karo na 73, kana ya shaida irin dadadden zumuncin dake tsakanin jama'ar Sin da Equatorial Guinea da ma daukacin al'ummar Afirka baki daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China